Amirka na neman wasu kasashe su yi gaban kansu a rikicin nukiliyar Iran
April 22, 2006Amirka ta ce ba ta da niyar jira har nan da wasu watanni don warware rikicin nukiliyar Iran ta hanyoyin diplomasiya. Gwamnatin Amirka ta ce kamata ya yi a dauki tsauraran matakai don kawo karshen shirin nukiliyar Iran. A cikin mako mai zuwa kwamitin sulhu na MDD zai saurari wani rahoto na ko Iran na biyayya ga bukatun kasa da kasa na dakatar da shirin tace sinadarin uranium. Karamin sakataren harkokin wajen Amirka Nicholas Burns ya ce idan kwamitin sulhun ya ki daukar mataki to daidaikun kasashe zasu yi gaban kansu wajen daukar matakan da suka dace ciki har da sanyawa Iran takunkumin sayar mata da makamai. Rasha wadda ke da ikon hawa kujerar naki, ta kawad da batun takunkumin har sai an samu kawakkwarar shaidar cewa Iran na aiwatar da wani shirin kera makaman nukiliya a boye.