1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na sa ido kan Turai da Iran

Yusuf Bala Nayaya MNA
January 28, 2019

A cewar fadar White House idanun Amirka na kan kasashen na Turai kan duk wani yunkuri na kawo karshen takunkumi da Amirkar ta maka wa Iran, kuma za su iya fuskantar dora laifi da ma tara.

https://p.dw.com/p/3CISg
USA Krise Shutdown l Präsident Trump verkündet vorläufige Aufhebung der Haushaltssperre
Hoto: Reuters/K. Larmarque

Gwamnatin Shugaba Donald Trump na Amirka ta bayyana cewa tana sa ido kan kokarin da kasashen Turai ke yi na ganin sun fitar da wata dabarar biyan kudade a harkokin kasuwanci da kasar Iran, ba tare da saba matakan takunkumi da kasar ta Amirka ta sanya wa Iran ba.

Mai magana da yawun Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa na samar da wata hanya ta daban a hulda da Iran, kuma nan ba da dadewa ba ne za a bayyana irin tsarin da aka yi.

Kafin dai a kai ga bayyana matakan na kasashen Turai da suka saba yadda aka saba hulda da kasar ta Iran, wani babban jami'i na Amirka ya bayyana cewa Amirkar za ta fadada takunkumin nata kan Iran kuma za ta dora alhaki ga duk wanda ya yi kokari na yin zagon kasa. Jami'in dai bai so a bayyana sunansa ba kan wannan batu.