Dawo da takunkuman MDD kan Iran
September 20, 2020Talla
Har yanzu Amirka na kan bakarta ta sake kakaba takunkumai ga gwamnatin Iran game da batun aikinta na bunkasa makamashin nukiliya, duk da yarjejeniyar da kasashen duniya suka cimma da Iran a shekarar 2015, da ma turjiyar da take fuskanta daga sauran kawayenta musamman ma na nahiyar Turai.
Sai dai a nata bangare gwamnatin Iran ta bakin ministan harkokin wajenta Mohammad Javad Zarif, ta bayyana a ranar Asabar da cewar batun sake kakaba takunkuman wani shaci fadi ne kawai na gwamnatin Amirka.