Fadar White House na turjiya ga kwamitin bincike
October 9, 2019Talla
Lauyan da ke kare Donald Trump ya bayyana a cikin wata wasikar da ya aikewa kakakin majalisar dokokin Amirka Nancy Pelosi cewa, ci gaba da binciken da 'yan jam'iyyar Demokrats ke hankorin yi kan batun matsin lambar da ake tuhumar shugaba Trump yayi ga takwaransa na Ukrain, domin ya binciki abokin hamayyarsa Joe Biden don samun wata dama ta daukar matakan tsige shugaban, baya da wani tushe da daga kundin tsarin mulki.