Amirka ta buƙaci China ta martaba haƙƙin 'yan Tibet
September 28, 2011Amirka ta yi kira ga kasar China da ta martaba haƙƙin al'umar yankin Tibet ta kuma biya musu buƙatunsa . Amirka ta yi wannan kiran ne bayan da wasu limaman addinin Budha biyu suka ƙona kansu da kansu- lamarin da ya ƙara dagula halin tsaro a wannan yanki. A cikin wata sanarwa da ta fitar ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta ce ya zamo wajibi China ta kare haƙƙin addini da yari da kuma al'adun al'umar Tibet . A ranar Litinin 26.09.2011 ne limaman na addinin Budha suka cunna wa kansu wuta domin nuna rashin amincewa da kasancewar wannan yanki a ƙarƙashin ikon China. Gwamnatin Amirka ta kuma buƙaci China da ta ba wa 'yan jarida da wakilan ƙasa da ƙasa ikon sa ido akan halin da ke wakana a lardin Sichuan inda aka gudanar da zanga-zanga a baya-bayan nan. Chinan dai ta gargagɗi Amirka da ta daina yi mata shisshigi a harkokinta na cikin gida.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi