1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta ce ana samun ci gaba a tattaunawar nukiliyar Iran

February 23, 2015

Sai dai wani jami'in diplomasiyar Amirka ya ce da sauran aiki gaba dangane da cimma wani kwakkwaran shiri mai ma'ana.

https://p.dw.com/p/1EgI3
Iran Atomstreit Kerry mit Zarif und Ashton 20.11.2014 Wien
Hoto: Reuters/L. Foeger

Wani babban jami'in Amirka ya ce ana samun ci gaba a tattaunawar da manyan jami'ai ke yi a kasar Switzerland a kan shirin nukiliyar Iran da ake takaddama kansa. Sai dai ya ce da sauran aiki gaba dangane da cimma abin da ya kira kwakkwaran shiri mai ma'ana. "An tattauna kan batutuwa masu muhimmanci masu kuma amfani", inji jami'in bayan ganawar da aka yi tsakanin ministan harkoin wajen Iran Mohammed Javad Zarif da takwaran aikinsa sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry a birnin Geneva. Jami'in ya kara da cewa a ranar Litinin mai zuwa za a gudanar da sabon zagayen wannan tattaunawa tsakanin Iran da kasashen Birtaniya da China da Faransa da Rasha da Amirka da kuma Jamus.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourrahmane Hassane