1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin matakan Amirka kan Iran

Gazali Abdou Tasawa
September 4, 2019

Gwamnatin Amirka ta sanar a wannan Laraba da daukar sabbin matakan ladabtarwa ga kasar Iran a fannin harakokin cinikin man fetur a bisa zargin tallafa wa kungiyoyin 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/3P19p
Öltanker Stena Impero
Hoto: Reuters/Wana/N. Tabatabaee

Gwamnatin Amirka ta sanar a wannan Laraba da daukar sabbin matakan ladabtarwa ga kasar Iran a bisa zarginta ta sayar da man fetur ga rundunar Qods ta kasar Iran wacce ita kuma ke taimaka wa kungiyar Hezbollah da sauran kungiyoyi da Amirkar kira na 'yan ta'adda a kasashen Labanan da Siriya.

 Sabbin matakan da baitulmalin kasar ta Amirka ya dauka sun shafi wasu kamfanoni jiragen dakon mai 16, da jiragen ruwan 11 da kuma mutane 10 wadanda Amirkar ke zargi gudanar da haramtaccen kasuwancin man fetur na kasar Iran.

 Kazalika kasar ta Amirka ta sanar da sanya ladar miliyan 15 na Dalar Amirka ga duk mutuman da zai samar mata da bayanai da suka shafi harakokin kudi na rundunar juyin juya hali da abiokiyarta ta Qods.

 Wanna mataki na Amirka na zuwa ne a daidai lokacin da kaasar ta Iran ta sanar da kara daukar matakan bijire wa yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da kasashen duniya a shekara ta 2015 tun daga yau ko kuma gobe Alhamis.