SiyasaGabas ta Tsakiya
Taliban: 'Yan Afghanistan sun sauka a Amirka
July 30, 2021Talla
Da ma dai tun da farko gwamnatin Shugaba Joe Biden ta yi alkawarin tsugunnar da dubban 'yan Afghanistan da suka yi wa sojojin Amirka aiki kuma suke tsoron kada a kai musu harin huce takaici a yanzu da Amirkan ta fara janye dakarunta a kasar.
A cikin wata sanarwa da Joe Biden ya fitar ya ce mutanen da suka fara sauka Amurka a wannan Jumma'a zangon farko ne na mutanen da Amirka ta kuduri aniyar dawo da su kasarta domin su rayu cikin kwanciyar hankali biyo bayan barazanar da suke fuskanta daga mayaka a Afghanistan.
Kawo yanzu dai kusan 'yan Afghanistan 20,000 ne da suka yi wa sojojin Amirka aikin tafinta ke bukatar Amirka ta ba su izinin shiga kasarta don tsira daga barazanar da suke fuskanta a cikin gida.