Amirka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran
May 8, 2018Talla
Shugaba Donald Trump na Amirka ya janye kasar daga cikin yarjejeniyar dakile nukiyar Iran, inda ya ce za a sake saka takunkumi kan kasar ta Iran.
Shugaba Trump ya zargi yarjejeniyar da rashin katabus da rashin samun wata nasara. Watanni 21 aka shafe ana tattauna wannan yarjejeniya tsakanin manyan kasashen duniya da kuma Iran, lokacin mulkin tsohon Shugaba Barack Obama na Amirka. Sauran kasashen da aka kulla wannan yarjejeniya tare da su sun hada da China, Rasha, Jamus, Faransa da Birtaniya.
Tuni Shugaba Hassan Rouhani ya gabatar da jawabi inda ya ce matakin na shugaban Amirka ya saba dokokin kasashen duniya. Sannan ya ce Iran za ta ci gaba da aiki da yarjejeniyar da sauran kasashe, kuma tuni kasashen Turai suka ce suna cikin yarjejeniyar.