Shirin sabunta dangantakan Amirka da Falasdinu
October 13, 2021Batun sake bude ofishin jakadanci a yankin Falasdinu da shirin nukiliyar Iran ne suka mamaye ganawar Sakataren harkokin wajen Amirka Anthony Blinken da takwarorinsa na Isra'ila da Hadaddiyar Daular Larabawa. Sakatare Blinken dai, ya ce shirin sake bude ofishin baya rasa nasaba da kokarin Amirka na sabunta dangantaka da Falasdinu.
A game da inda aka kwana kan shirin nukiliyar Iran kuwa wanda ya kasance babban damuwan Isra'ila, Mista Blinken ya nuna mahinmancin amfani da lokaci a cimma matsaya, sai dai yayi gargadi kan daukar duk wani mataki muddun Iran ba ta bayar da hadin kai ba a kokarin da ake na son ganin na cimma matsaya. A na shi bangaren Yair Lapid na Isra'ila, yayi barazanar amfani da karfi muddun Iran ba ta sauya matakinta ba.
Shirin nukiliyar Iran da ake fargabar na tattare da hadura ga kasashe makwabtanta dama duniya baki daya, ya ci gaba da haifar da tsamin dangantaka a tsakaninta da sauran kasashen duniya.