Amirka ta gindaya sharudda don sabunta yarjejeniyar Iran
May 22, 2018
Sharudda 12 masu wuyar aiwatarwa da Sakataren harkokin wajen Amurka na Mike Pompeo, ya gindayasu kafin a sabunta yarjejeniyar nukiliya da Iran, sun kunshi matakan karya bakalin kasar ta Iran a bangaren sojoji da karya bakalin tasirinta na diplomasiyya a yankin. Pompeo ya kuma ja kunnen kasashen Turai da kamfanoninsu da ke son ci gaba da hulda da Iran, wadandan ya ce idan suka bijire wa matakin na Amurka, to kuwa su ma za su yaba wa aya zaki.
Tuni dai shugaban Iran, Hassan Rouhani, wanda ya nemi kasashen Turai da su karfafa alakarsu ta kasuwanci da ita,ya yi watsi da wannan barazana.
A yayin da kasashen Saudiyya da Daular Larabawa da Baharain suka siffanta sharuddan da wadanda aka jima ana jira, suka kuma wajaba da a aiwatar da su sau da kafa. Ita kuwa Shugabar kula da harkokin kasashen waje ta kungiyar Tarayyar Turai, Federica Mogherini cewa ta yi "Babu abin da zai hana kasashen kungiyar ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar Iran, duk da takunkuman da Amurkan ke barazanar sake kakaba wa kamfanonin kasashen na Turai a kan Iran.”
Sakataren harkokin wajen kasar Birtaniya Boris Johnson ya siffanta sharuddan da na gagara badau, yana mai nuna takaicinsa da yin fatali da tsohuwar yarjejeniyar da Amirka ta yi, wacca ya ce ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya da habakar hada-hadar kasuwanci.