1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta haramta sayen kaya daga China

Binta Aliyu Zurmi
August 8, 2019

Ofishin gudanarwa da kasafin kudi na fadar shugaban Amirka ya haramta sayen kaya na wucin-gadi daga kamfanoni biyar na China ciki har da Huawei.

https://p.dw.com/p/3NWjM
China Shenyang | Hauwai Geschäft
Hoto: picture-alliance/dpa/Imaginechina/Z. Wenkui

Haramcin na daga cikin matakan tsaro da Amirka ta yanke a shekarar bara wanda su ka yi tir da kayayaki malalkar kamfanin Huawei wanda ke zama na daya a duniya a fanin sadarwa. Washinton dai na zargin kamfanin ne da satar bayanai na sirri, a yayin da kamfanin ya musanta zargin da kuma dagewa kan cewa gwamnatin China bata da iko a kamfanin.