1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta janye daga hukumar Unesco

Gazali Abdou Tasawa
October 12, 2017

Kasar Amirka ta sanar da janyewa daga hukumar kula da raya ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO a bisa zarginta da kasancewa mai kyamar kasar Isra'ila.

https://p.dw.com/p/2lkc5
UNESCO Konferenz in Paris
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Euler

Kasar Amirka ta sanar da bisa zargin hukumar da kasancewa mai kyamar kasar Isra'ila. Ofishin ministan harakokin wajen kasar ta Amirka ne ya sanar da wannan mataki a cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Alhamis inda ya kuma bayyana bukatar ganin an sake wa hukumar ta Unesco fasali. 

Dama dai tun a watan Yulin da ya gabata Amirkar ta sanar da sake duba dangantakarta da hukumar ta Unesco bayan da ta bayyana tsohon birnin Hebron na Yammacin kogin Jodan da Isra'ila ta mamaye a matsayin daya daga cikin kadarorin gado na duniya. 

Tun a shekara ta 2011 ne dai dama Amirka ta dakatar da baiwa hukumar ta Unesco tallafin kudi bayan da ta amince kasar Palasdinu a jerin kasashe mambobinta, sai dai ta ci gaba da halartar zaman kwamitin zartarwa na hukumar mai mambobi 58 kafin yanzu ta sanar da janye wa daga cikinta baki daya. Isra'ilar ma dai ta sanar da soma shirye-shirye na janyewarta daga cikin wannan hukuma ta Unesco.