1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta kai hari ta sama kan wani taro a Siriya

March 18, 2017

Kasar Amirka ta amince da kai wani hari kan wani taron 'yan kungiyar al-Qaeda da aka ce ya tarwatsa masallaci da mutane a ciki.

https://p.dw.com/p/2ZTSz
Syrien Krieg - Kämpfe in Daraa
Hoto: Getty Images/AFP/M. Abazeed

Gwamnatin kasar Amirka, ta amince da kai hari ta sama kan wani taro na kungiyar al-Qaeda a kasar Siriya, sai dai ta ki amincewa afkawa masallaci da shaidu suka ce mutane 49 sun mutu.

Kamar dai yadda kungiyar kare hakkin bil Adama ta Syrian Observatory for Human Rights ta nunar, akasarin wadanda suka mutun dai fararen hula ne. Amirkar ta kai harin ne a kauyen Al Jineh da ke lardin arewacin Aleppo na kasar ta Siriya.

Wani wakilin kamfanin dillacin labaran AFP da ya ziyarci yankin jiya Juma'a, ya ce akwai masallatai biyu da harinn ya shafa, inda tsoho daga cikinsu ya lalace, yayin da wani sabo kuwa ya ruguje kwata-kwata. Akwai ma wasu mutanen kimanin 30 da ke karkashin rusasshen masallacin.