1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden ya sa takunkumi kan 'ya'yan Putin

Abdul-raheem Hassan
April 6, 2022

Gwamnatin Amirka ta sake sanya sabbin takunkumi kan kasar Rasha, a wannan karo ya shafi 'ya'yan Shugaba Vladimir Putin mata guda biyu da tsohuwar matarsa da wasu manyan jami'an kasar da wasu bankuna masu zaman kansu.

https://p.dw.com/p/49YsZ
Kombobild Katerina Tichonowa, Wladimir Putin, v Maria Vorontsova
Hoto: Eastnews/imago/Mikhail Klimentyev/SPUTNIK /AFP/Dmitry Feoktistov/TASS/picture alliance

Wannan mataki na gwamnatin Wahington ana ganinsa a mastayin wani yunkuri na karya tattalin arzikin Rasha kan mamaye Ukraine da take yi. Shugaba Joe Biden ya danganta karuwar takunkumin kai tsaye ga shaidun da ke nuna cewa sojojin Rasha sun kashe fararen hula da gangan a Bucha, wani gari da ke wajen Kyiv babban birnin kasar Ukraine.

Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Rasha tun da fari ta karyata zargin cewa ta aikata kisan gilla da gangan a garin Bucha, ta kuma kara da cewa zargin na iya rusa fatan da ake da shi na cimma yarjejeniyar zaman lafiya.