Amirka ta kara jaddada goyon bayanta ga kasar Masar
February 12, 2018Talla
Rex Tillerson ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da takwaransa na kasar Masar daga nan sai ya kara da cewar Amirka ba za ta gajiya ba wajen ganin an gudanar da zabubbuka a kasashen Larabawa bisa cancanta,kamar yadda kasar ta dauki aniyar gani ta maido da zaman lafiya tsakanin kasashen Falasdinu da Isara'la. Duk kuwa da cewar Donald Trump ya ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, a karshe ya roki al'ummar kasar Masar da su ci gaba da goyon bayan Amirka don maido da tsaro kasar.