1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta karyata zargin da kasar Turkiyya ta yi ma ta

Zulaiha Abubakar
February 15, 2018

Sakataren tsaron kasar Amirka  Rex Tillerson ya ce zargin da Turkiyya ta ke yi wa Amirka a kan ba mayakan Kurdawa da ke kasar Siriya kayan yaki batu ne mara tushe.

https://p.dw.com/p/2sldf
US-Außenminister Rex Tillerson nimmt an einer Pressekonferenz mit dem britischen Außenminister Boris Johnson in London teil
Hoto: Reuters/T.Melville

Ya kuma kara da cewar Amirka ta maida hankali ne a kan ganin ta kawo karshen kungiyar ta'addanci ta IS a  Siriya yayin da ana ta bangaren kasar Turkiyya ta dauki aniyar ganin Kurdawan ba su samu wata kariya daga ko wane bangare ba,lamarin da ya sanya ta kaddamar da wani harin sojoji a yankin Afrin don fatattakar Kurdawa daga kan iyakar ta da kasar ta Siriya. Rex Tillerson ya kara da cewa Amirka ta gudanar da wasu tarurruka da kasashen Turai a kan batun makami mai linzami a kasar Iran ko da yake har yanzu akwai sauran aiki.