1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

AGOA: Amirka ta kori kasashen Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 24, 2021

Amirka ta soke damar da Habasha ke da ita ta yin kasuwanci mara shinge a tsakaninsu, sakamkon rikicin yankin Tigray.

https://p.dw.com/p/44oZX
Äthiopien North Wollo | Tigray Konflikt zerstörte Fahrzeuge
Rikicin na Tigray dai, ya daidata yankin baki dayaHoto: Seyoum Getu/DW

Wannan rikici na sama da shekaraguda dai, ya halaka mutane da dama tare da jefa wasu miliyoyi cikin halin taskun rayuwa da yunwa. Amirkan ta bayyana cewa za a kori kasar Habashan da ke yankin Kahon Afirka daga cikin tsarin na kasuwanci mara shinge na AGOA, daga ranar daya ga watan Janairun badi. Matakin dai bai zo da mamaki ba, ganin cewa gwamnatin Shugaba Joe Biden ta sha alwashin daukarsa tun cikin watan Nuwambar da ya gabata. Amirka da sauran kawayenta, sun nunar da cewa akwai rahotanni masu inganci da ke nuna yadda mahukuntan na Adis Ababa ke take hakkin dan Adam yayin da suke fafatawa da mayakan yankin na Tigray. Kasashen Guinea da Mali da ke yankin yammacin Afirka ma dai, na daga cikin wadanda Amirkan ta kora daga tsarin na AGOA.