An gano mai taimaka wa Iran da kayan kera makamai
March 30, 2022A yayin da ake kokarin cimma yarjejeniya a tsakanin Iran da wasu manyan kasashen duniya, Amirka ta sake sanar da kakaba wa wasu manyan kamfanonin Mohammad Ali Hosseini, wani attajirin kasar ta Iran takunkumi bisa zargin hannu a sayo kayayyakin da gwamnatin Tehran ke bukata a shirin nukiliyarta.
Amirka ta ce, duk da tattaunar da ake ci gaba da yi don ganin Iran da kasashen sun cimma matsayar koma wa yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 2015, hakan baya nufin za ta zura idanu a ci gaba da sarrafa makaman da yammacin duniya ke nuna damuwa a kansa.
A farkon wannan watan na Maris, an zargi Iran da amfani da wani nau'in makami mai linzami a Irak da kuma mara wa mayakan Houthi na Yemen baya a hare-haren da suka kai cibiyoyin man Saudiya, wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake daf da cimma yarjejeniyar da tsohon shugaban na Amirka Donald Trump ya soke a shekarar 2018.