Amirka ta mai da martani ga baraznar Iran
December 29, 2011Kasar Amirka ta mai da martani game da barazanar da Iran ta yi cewa za ta toshe mashigin ruwan Hormuz da ke da muhimaci ga aikin dakon man fetur a duniya in har aka dora mata takumkumin sayar da manta a kasuwannin duniya. Amirka ta ce ta girke sojojin ruwanta a wannan yanki na mashigi ruwan da ke tsakanin Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amirka ya jadadda tura sojojin zuwa wannan yanki. To amma ya kara da cewa ya yi imanin za a yi sara ana duba bakin gatari wajen shiga takun saka da Iran. Ita dai Iran ta taba yin irin wannan barazana a wani lokaci can baya. Mataimakin Shugaban Iran, Reza Rahimi shi ne ya yi baraznar toshe mashigin ruwan in har kasahen yamma suka dora wa kasarsa karin takunkumi saboda shirinta na nukiliya- baraznar da shugaban rundunar ruwan Iran ya jadadda. Kungiyar Tarayar Turai da Jamus dai sun bayyana aniyarsa ta aza wa Iran karin takunkumi.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu