1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta nemi kawo karshen rikicin Ukraine

April 22, 2014

Amirka ta nemi Rasha ta janye dakaru kan iyakar Ukraine

https://p.dw.com/p/1BmKd
Hoto: Reuters

Gwamnatin kasar Ukraine ta ce ayyukan 'yan aware masu goyon bayan kasar Rasha suna tarnaki wa yajejeniyar nema kawo karshen zaman tankiya cikin yankin gabashin kasar ta Ukraine. Wannan dai dai lokacin da Amirka ta yi sabon alkawari na bai wa kasar Dala bilyan 50, domin gudanar da sauye-sauyen tattalin arzikin da siyasa.

Mataimakin Shugaban kasar ta Amirka Joe Biden ya bayyana haka yayin ziyarar aiki da yake yi a kasar ta Ukraine. Biden ya kuma tilas Rasha ta janye tankokin yaki daga kan iyakar Ukraine. Sannan ya ce Rasha za ta zama saniyar ware, muddun ta ci gaba da barazana wa Ukraine.

Firamnistan kasar ta Ukraine Arseny Yatseniuk, ya ce ayyukan dakarun Rasha na musamman na tarnaki bisa shirye-shiryen zaben Shugaban kasa na ranar 25 ga watan gobe na Mayu.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu