Amirka ta sake magana kan sojojinta da ke Siriya
January 6, 2019Talla
Hukumomin Amirka sun ce batun janye dakarun kasar daga Siriya, zai dogara ne da nasarar kakkabe mayakan IS da ma samun tabbaci daga Turkiyya kan makomar mayakan Kurdawa.
Mashawarcin Shugaba Donald Trump kan harkokin tsaro, John Bolton, wanda ya bayyana hakan a ranar Lahadi, ya ce magana ta gaskiya babu jadawali kan janyewar dakarun na Amirka a dai halin da ake ciki.
Jami'in ya fadi hakan ne a wata ziyararsa a Isra'ila, lokacin da yake tabbatar wa babbar kawar Amirkar wannan batu.
Cikin watan Disambar da ta gabata ne dai, Shugaba Trump, ya sanar da shirin janye sojoji 2000 a yankin arewa maso gabashin Siriyar, saboda abin ya ce na karya lagon kungiyar IS da aka yi.
Sai dai fa bai sami amincewar manyan kasashen yamma ba.