Amirka ta sanya rundunar sojin Iran cikin kungiyar ta'adda
April 8, 2019Talla
Matakin na Shugaba Trump wani yunkuri ne na kara tsananta wa Iran din, wanda ka iya dagula harkokin diflomasiyyarta a yankin kasashen larabawa.
Wannan ne karo na farko da Amirka ke ayyana gwamnatin wata kasa a matsayin kungiyar ta'adda a duniya.
Tuni kuwa gwamnatin kasar Bahrain, ta yi marhabin da matakin na Amirka.
Matakin ya kuma kakaba takunkumin janye kadarorin da rundunar mayakan juyin juya halin kasar ta Iran ka iya mallaka a wuraren da Amirka ke da iko, da ma katse duk wata hulda da ita.
Sai dai gwamnatin Iran, ta yi barazanar rama wa kura aniyarta.
A shekara ta 1979 ne dai aka kafa rundunar juyin juya halin na Iran, inda take karbar umurni kai tsaye daga jagoran addini na kasar.