1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alwashin taka burki kan makaman Iran

Yusuf Bala Nayaya
February 8, 2019

Sojojin juyin-juya halin Iran sun bayyana sabon makami mai linzami da idan an harba zai kai kilomita 1,000.

https://p.dw.com/p/3Cykr
Iran: Rakete Dezful
Hoto: picture-alliance/AP/Sepahnews

Kasar Amirka ta bayyana a ranar Alhamis cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta matsa lamba kan kasar Iran ga batun shirinta na makami mai linzami, abin da ke zuwa bayan da Jamhuriyar Musulunci ta bayyana sabon makamin da ta kera kwanaki bayan ta yi gwaji na makami mai linzami.

Sojojin juyin-juya halin Iran sun bayyana sabon makami mai linzami da idan an harba zai kai kilomita 1,000 kamar yadda kamfanin dillancin labari na Sepah ya ba da rahoto.

Wannan dai shi ne karo na baya-bayan nan da sojojin na Iran suka sake bayyana irin karfin makaman da suke da su bayan kuwa kasar ta yi biki na cika shekaru 40 na juyin-juya halin Islama adaidai lokacin da aka shiga yanayi na takun saka da kasar Amirka.