1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta shirya tsare-tsare kan Gabas ta Tsakiya

January 24, 2020

Shugaba Donald Trump na kasar Amirka, ya ce cikin 'yan kwanakin da ke tafe ne zai bayyana sabbin tsare-tsaren da za su samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/3WkIk
Weltwirtschaftsforum 2020 in Davos | Donald Trump, Präsident USA
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Vucci

Shugaba Donald Trump na fadin hakan ne yayin da wasu manyan 'yan siyasar Isra'ila ke shirin ziyartar fadar White House cikin makon da ke tafe.

Shirin dai kamar shugaban ya nunar, na da manufar kawo karshen rikice-rikicen da aka kwashe shekaru ana yi a tsakanin Ira'ila da kuma Falasdinu, musamman ma matsayin Birnin Kudus.

Sai dai fa kadan ne daga cikin shirye-shiryen suka fito fili, ko da yake an bayyana wani daga cikin abin da ya shafi tattalin arziki.

Kuma kamar yadda ya fito, surukin shugaban na Amirka ne wato Jared Kushner, ya tsara kusan dukkanin abubuwan da suka danganci hakan.

A ranar Talata mai zuwa ne dai Amirkar za ta bayyana tsare-tsaren.