Aiyukan dakarun Afirka kan al-Shabab na kyau
July 27, 2015Shugaba Barack Obama na Amirka ya bayyana cewa yadda dakarun sojan kawancen Afirka na AU da dakarun sojan Somaliya ke kara matsa lamba kan mayakan al-Shabab abin a yaba ne, sai dai ya kara cewa dole ne a sake dagewa kan wadannan mayaka masu tada kayar baya.
Da yake jawabi a birnin Addis Ababa na kasar Habasha shugaba Obama ya ce mayakan na al-Shabab babu abin da suka sanya a gabansu sai halakar da jama'a da lalata gine-gine.
A cewar shugaba Obama kasar ta Habasha na da babbar barazana da ke a gabanta, abin da ya sanya dole su tashi tsaye dan fiskantar wannan kalubale.
"Hadin kanmu a bangaren tsaro shi ne mu tunkari masu tsatstsauran ra'ayi . Kasar Habasha na fiskantar babban kalubale sannan tallafin da take bayarwa wajen yaki da mayakan na al-Shabab cikin dakarun kasashen Afrika ya yi baya, amma kamar yadda Firaministan kasar ya gani a ranar Lahadi a harin birnin Mogadishu babu abinda mayakan suka sa gaba sai ganin suna kwararar da jini da lalata wurare abinda ya sa muke da aiki ja a gabanmu."