Amirka ta yi tir da hukuncin kisa a Masar
March 26, 2014Kotun da ke sauraron karar mutanen nan 700 a Masar ta dage shari'ar tasu zuwa ranar 28 ga watan Afirilu mai zuwa. An dai dage shari'ar mutanen da suka hadar da shugaban kungiyar 'yan uwa Musulmi Mohammed Badie wanda kuma ake tsammanin za su fuskanci hukuncin kisa. Kwana guda dai kafin gurfanar da su gaban kuliya, kotun ta yanke wa wasu mutane sama da 500 hukuncin kisa, hukuncin kuma da yake fuskantar suka daga ciki da wajen kasar ta Masar. Tuni dai Amirka ta yi gargadin cewa hukuncin zai iya shafar dangantakarta da Masar musamman ta fuskar talallafin da take bai wa sojojin Masar din. Tun dai bayan da sojoji suka kifar da zababbiyar gwamnatin dimokaradiyya ta Masar din karkashin jagorancin Mohammed Morsi 'yan adawar kasar ke fuskantar muzgunawa da kuma kokarin murkushesu da karfin tuwo.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal