1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta kauracewa Olympics na China

Abdul-raheem Hassan
December 7, 2021

Washington za ta kaurace daga wasannin Olympics na kasar China a shekarar 2022 saboda zargin take hakkin dan Adam, Amirka ta ce ba za ta aike da tawagar diflomaisiyya ba amma za ta mara wa 'yan wasanta baya 100 bisa 100.

https://p.dw.com/p/43utk
China | Vor den Olympischen Winterspielen in Peking
Hoto: Mark Schiefelbein/AP/picture alliance

Amirka ta yanke shawarar katse diflomisiyya kan harkokin wasannin Olympics saboda zargin kasar China kisan kare dangi kan Musulman Uygur a yankin Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar.

Sai dai a wani martani na farko da kasar Sin game da matakin Amirka na neman ragewa gasar armashi, ofishin jakadancin China a Washington ya ce kaurace wa gasar ba zai yi wani tasiri ba kan wasannin ba, haka nan babu wanda zai damu da ko Amirka ta aike da tawagar diflomasiyya.

Kungiyoyin kare hakkin jama'a da 'yan siyasa a Amirka sun yi maraba da wannan mastayi, matakin da ke zuwa a lokacin da Shugaba Joe Biden na Amirka ke fuskantar matsin lamba a cikin gida kan take hakkin da ake zargin China.