1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta tsayawa Taiwan

Abdul-raheem Hassan
October 22, 2021

Shugaba Biden ya ce za ta tsaya kai da fata na ganin ta kare tsibirin Taiwan daga yunkurin da China ke yi na mamaya. Biden ya fadi haka ne a wani shirin talabijin na CNN.

https://p.dw.com/p/420n9
USA Präsident Joe Biden
Hoto: Susan Walsh/AP Photo/picture alliance

Shugaba Biden ya ce kasashen China da Rasha da sauran kasashen duniya suna sane da karfin sojin Amirka a tarihin duniya, ya kuma ce su yi kuka da kansu idan suka yi wa Amirka katsalandan a harkokinta na ciki da waje.

Matsayar gwamnatin Amirka na tsaya wa Taiwan, na zuwa ne bayan da China ta fito fili ta nuna bukatar hadewa da Taiwan a cikin ruwan sanyi ko ta tsiya nan ba da jimawa ba, matakin da ya haifar da martanin tir daga hukumomin Taiwan.