1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta saka hannayen jari a Afirka

Binta Aliyu Zurmi MAB
December 15, 2022

Shugaba Joe Biden ya yi wa kasashen Afirka alkawarin tallafin biliyoyin kudi domin inganta fannin lafiya da samar da ababen more rayuwa da samar da fasahar kimiya da kuma inganta fanini kasuwanci a nahiyar.

https://p.dw.com/p/4L1NI
USA US-Afrika-Gipfel der Staats- und Regierungschefs Joe Biden
Hoto: Michael Reynolds/Pool via CNP/picture alliance

Shugaban na Amirka ya yi wannan shelar ne a taron koli na shugabannin Afirka da Amirka wanda ake kammalawa a birnin Washington DC a wannan Alhamis. Biliyan 55 na dalar Amirka ne Biden ya ce gwamnatinsa za ta zuba hannayen jari a Afirka a nan da shekaru 3 da ke tafe, a kokarin dakile tasirin Chaina da Rasha a nahiyar. Dama taron na kwanaki uku na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Chaina take neman tsere wa Amirka a yawan saka hannayen jari a Afirka.

Shugaba Biden ya ce Amirka a shirye ta ke na tallafawa Afirka a duk hanyoyin da za su sami ci gaba, inda ya kara da cewar ci gaban Afirka ci gaban Amirka ne da ma duniya baki daya. A karshen taron Shugaba Biden ya yi alkawarin kai ziyara ga kasashen da ke Kudu da Hamada Sahara nan bada jimawa ba.