Sabon firaiministan Irak ya kama aiki
May 7, 2020Talla
Firaminista Mustafa Kadhimi mai shekaru 53 ya taba rike mukamin shugaban hukumar leken asirin kasar, da dama daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar sun tsoratar game da nadin Mustafa Kadhimi a matsayin firaministan sakamakon alakar sa da kasar Amirka. Kasar ta Irak ta afka rikicin siyasa bayan tsohon firaiminista ya sauka daga mukaminsa a bara biyo bayan ballewar zanga-zanga a kasar sakamakon rashin aikin yi tsakanin al'umma da kuma zargin masu rike da mukaman gwamnati da arzurta kan su da kudaden kasar.
Sabon Firaminista Kadhimi zai kama aiki a wannan Alhamis din, a lokacin da Irak ke fama da matsalar karyewar tattalin arziki da yaduwar cutar Coronavirus a fadin kasar da kuma billar zanga-zanga a yankuna daban daban na kasar.