1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty: Karuwar take hakkin jama'a a Nijar

Salissou BoukariJune 24, 2016

Kungiyar kare hakkin jama' ta kasa da kasa ta Amnesty ta yi tsokaci kan hukuncin da aka yanke wa wani dan rajin kare hakin dan Adam da karfafa demokaradiyya a Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/1JCHx
Amnesty international
Hoto: picture-alliance/dpa/W.Kumm

Kungiyar mai kare hakkin jama'a ta kasa da kasa ta ce wannan hukunci na watanni shida na daurin talala da aka yanke wa Abdoul Moumouni ya nunar cewa, a halin yanzu dai 'yancin fadar albarkacin baki na kara fuskantar babban kalubale ga al'ummar kasar ta Nijar.

Amnesty International dai ta ce laifin da ake zargin Moumouni da aikata wa da ya danganci kulla makarkashiya dai bai tabbata ba, amma kuma yanke masa wannan hukunci na kason waje har na tsawon watanni shida, ya tabbatar da matsin lambar da hukumomin na Nijar ke yi kan 'yancin fadar albarkacin baki.

Shi dai Abdoul Moumouni Ousmane da ke shugabancin wata kungiya da ake kira CADDRH da ke fafutukar kare demokaradiyya da hakkokin bil-Adama a kasar ta Nijar, ta shafinsa na Facebook, ya soki lamirin shugaban kasar na Nijar Issoufou Mahamadou kan yadda yake tafiyar da harkokin yaki da 'yan kungiyar Boko Haram a yankin jihar Diffa, bayan harin da aka kai a garin Bosso da ya hallaka sojoji kasar da dama.