1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty: Matsalolin cin zarafi da suka faru a 2022

Suleiman Babayo
March 28, 2023

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta duniya Amnesty International ta ce cin zalin da Rasha ke yi wa Ukraine da dirar mikiya akan masu zanga zanga a Iran su ne mafi kamarin cin zarafin al'umma a 2022

https://p.dw.com/p/4POLf
Iran Protest in Rom
Hoto: Gregorio Borgia/AP Photo/picture alliance

Rahoton ya nuna shekarar 2022 ta zama lokacin da aka fi tsere wa rikice-rikice a duniya, kuma lokacin da aka samu milyoyin mutane da suka fita zanga-zangar neman kare hakkinsu saboda barazana da suke fuskanta. Kungiyar Amnesty International ta tattara bayanai game da laifukan da aka aikata ga dan Adam a kasashe 156 da suka hada da aikin dakarun Rasha a kasar Ukraine.

Janine Uhlmannsiek mai ba da shawara ga kungiyar Amnesty Intertional a kasashen Turai da tsakiyar Asiya da ke Jamus ta bayyana cewa kutsen da Rasha ta yi a Ukraine ya yi mummunar tasiri kan hulda tsakanin kasashen dunyia:

Janine Uhlmannsiek mai ba da shawara ga kungiyar Amnesty a kasashen Turai
Janine Uhlmannsiek mai ba da shawara ga kungiyar Amnesty a kasashen TuraiHoto: Sarah Eick/Amnesty International

"Kutsen da Rasha ta kaddamar kan kasar Ukraine ya yi illa ga kudirorin Majalisar Dinkin Duniya tare da janyo karin laifuka na kasa da kasa."

A kasashe 62 na duniya gwamnatoci sun dauki matakin dakile zanga-zanga da haduwar mutane, sannan a wasu kasashe 79 an kama 'yan gwagwarmaya ba tare da sun aikata wani laifi ba tare da gana musu azaba. Kasar Rasha bayan ta kaddamar da kutse kan Ukraine tare da aikata laifuka yaki. 

"Amnesty tana da shaidar yaro dan shekara 11 da aka raba da mahaifiyarsa. Sannan mun tattara bayanan yara da aka  yi safararsu wadanda suke tafiya ba tare da iyayensu ba daga Mariupol zuwa Donetsk"

Kwararriyar ta kungiyar Amesty ta kara da cewa matakan siyasa da aka dauka a Rasha shi ne yadda cikin hanzari yaran aka mika su ga iyalan da suke neman yaran da za su rike, gwamnatin Rasha tana kuma musgunawa 'yan kasar da suke adawa da yakin da ta kaddamar kan Ukraine.

Katja Müller-Fahlbusch kwararriya kan kasashen Gabas ta Tsakiya da arewacin Afirka
Katja Müller-Fahlbusch kwararriya kan kasashen Gabas ta Tsakiya da arewacin AfirkaHoto: Sarah Eick/Amnesty International

A Iran mutuwar Mahsa Amini a hannun jami'an tsaro ta tayar da kura ganin zanga-zangar da ta biyo baya, inda gwamnatin ta yi amfani da karfin da ya wuce kima.

Katja Müller-Fahlbusch kwararriya kan kasashen Gabas ta Tsakiya da arewacin Afirka a kungiyar Amnesty International da ke Jamus, ta nunar da cewa kasashe suna iya shawo kan matsalar da ake fuskanta a Iran muddin za a daga-murya:

"Game da Iran, a zahiri akwai al'umma da ta saka matsin lamba. Sai dai an shiru a bangaren diflomasiyya, misali yadda ake daure 'yan kasar da suke da takardun tafiya na wasu kasashe ba tare da an dauki wani mataki ba. Mene ne taimako, shi ne matsin lamba daga mutane da zai nuna irin laifuka na siyasa da ake aikatawa. Haka zai kara iren abin da Jamhuriyar musulunci ta Iran za ta fuskanta bisa haka."

Sojojin da ke mulki a Mymmar suna ci gaba da cin zarafin mutane haka rikicin Habasha ya yi tasirin kan zaman kasar.