1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta zargi sojan Siriya da kai hare-hare a asibitoci

Abdoulaye Mamane Amadou
May 11, 2020

Kungiyar Amnesty International ta zargi rundunar sojan Siriya da kawayenta da kaddamar da wasu hare-hare kan makarantun boko da asibitoci a yankin Arewa maso yammacin kasar

https://p.dw.com/p/3c0h4
Syrien Idlib Offensive türkische Truppen Rebellen
Hoto: Getty Images/AFP/B. Alkasem

A cikin wani rahoton mai shafi 40 da kungiyar ta fitar, Amnesty International ta zargi sojan Siriya da kaddamar da hare-hare kimanin 18 kan fararen hula da basu san hawa ba su san sauka ba a asibitoci ko makarantun boko, daga farkon watan Mayun 2019 zuwa tsakiyar watan Fabrairun wannan shekrara.

Kungiyar ta ce rahotonta ya ta'alaka ne kan wasu cikakkun bayanai da ta samu daga likitoci da 'yan gudun hijira da malamai hakan da wasu daidaikun ma'aikata na Majalisar Dinkin Duniya.