SiyasaAfirka
Amnesty: Hukuncin kisa na karuwa a Masar
December 2, 2020Talla
Kungiyar Amnesty International, ta soki gwamnatin kasar Masar bisa laifin aiwatar da hukuncin kisa da tayi kan gomman mutane a watanni biyu da suka gabata. A sanarwar da ta fitar, ta ce kusan mutum sittin aka kashe a tsakanin watannin Oktoba da Nuwambar da suka gabata, cikinsu har da mata, ana yanke musu hukuncin duk da tababan da ake kan laifukan da ake tuhumarsu.
Wani abun damuwa dai, shi ne yawan wadanda ake tsare da su yanzu a gidan yari, da su da iyalansu ba su da masaniya kan hukuncin da ke jiransu na kisa, mataki ne da ya tauye hakkin kowanne bil'adama injin´kungiyar. Lamarin ya fi shafar 'Yan jarida da masu fafutuka da lawyoyi da malaman jami'oi da 'yan siyasa da gwamnati ke zargi bisa laifuka na sukar muradun gwamnati.