1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta Zargi Pakistan da laifin take hakkin bil adama

September 29, 2006
https://p.dw.com/p/Bui5

Kungiyar kula da kare hakkin bil adama ta Amnesty ta zargi kasar Pakistan da laifin tsare daruruwan wadanda take zargi da taadanci,ciki kuwa har da baki tare tana mai kai su gidajen yari na boye ko kuma mika su ga hukumomin Amurka domin ta amshi kudi daga hukumomin na Amurka.

Cikin rahotanta da ta fito da shi, Amnesty tace kasar Pakistan abokiyar kawancen Amurka tana take hakkin bil adama da suan yaki da taaddanci.

Wannan zargi dai ya zo ne kwanaki kadan bayan shugaban kasar Pakistan Parvez Musharraf cikin wani jawabi da yai,ya baiyana cewa sun kame yan alqaeda 689 kuma sun mika 369 daga cikinsu ga hannun Amurka hakazalika Musharraf yace sun samu miliyoyin daloli.

Babban direktan bincike na kungiyar ta Amnesty Claudio Cordone yace yawancin wadanda Pakistan take tsarewa tana kai sune gidajen yari na asiri,ciki har da Guantanamo da kuma Bagram a arewacin birnin Kabul.