Amsoshin Takardunku 09.10.2024
October 9, 2024Hasan Nasrallah na daya daga cikin jagororin Gabas ta Tsakiya da ya fi jawo cece-kuce, inda a yayin da wasu ke daukan sa a matsayin gwarzo da ke yaki da mulkin danniya da mamaya, wasu kuma na daukansa a matsayin dan ta'adda da kasar Iran ke amfani da shi wajen cimma muradunta. Shi dai Hassan Nasrallah da aka haifa a ranar 31 ga Agusta 1960 a Bourj Hammoud, wata unguwar gabashin Beirut . ya kasance malamin addinin Musulunci na Lebanon kuma dan siyasa, wanda ya rike mukamin shugaban kungiyar Hezbollah ta 'yan Shi'a da ke gagwarmaya da makamai daga 1992 har zuwa lokacin da aka kashe shi a wani harin da Isra'ila ta kai a ranar 27 ga watan Satumban 2024.
A karkashin jagorancin Nasrallah ne, kungiyar Hezbollah ta samu makaman roka, wanda hakan ya ba wa 'ya'yan kungiyar damar kai hari a arewacin Isra'ila. Hasali ma dai, bayan da Isra'ila ta sha fama da munanan hare-hare na tsawon shekaru 18 da ta yi a kudancin Lebanon, ta janye dakarunta a shekara ta 2000, wanda hakan ya kara wa kungiyar Hezbollah farin jini sosai a yankin, da kuma karfafa matsayin Hezbollah a cikin kasar ta Lebanon. Ita dai Hezbollah ta yi ta kambama sunan Hassan Nasrallah a kafafen yada labarai a matsayin mai kwarjini, duk da cewa ya samu rauni daga baya. Wata rawa da kungiyar Hezbollah ta taka a harin kwanton bauna a kan dakarun Isra'ila a kan iyakokin kasar da suka kai ga yakin Lebanon na 2006 ya fuskanci suka, duk da cewa ya kawo karshen yakin a matsayin nasara ta Lebanon da Larabawa.