1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Amurka da kawayenta zasu gabatar da daftarin karshe kan Gaza

October 18, 2024

Shugaba Joe Biden na ziyararsa ta karshe kafin sauka daga kan karagar mulkin Amurka a nan Jamus domin tattaunawa da shugabannin Turai kan kawo karshen yakin Gaza bayan halaka shugaban kungiyar Hamas Yahya Sinwar.

https://p.dw.com/p/4lw8U
Shugaban Amurka Joe Biden yayin tattaunawa da manema labarai jim kadan da saukarsa a filin jiragen sama na Berlin-Brandenburg na tarayyar Jamus
Shugaban Amurka Joe Biden yayin tattaunawa da manema labarai jim kadan da saukarsa a filin jiragen sama na Berlin-Brandenburg na tarayyar JamusHoto: Elizabeth Frantz/REUTERS

Biden ya jinjinawa Isra'ila kan halaka Yahya Sinwar wanda Isra'ila ke nema ruwa a jallo bisa zargin kitsa harin ranar 7 ga watan Oktoba. Shugaban na Amurka ya ce kashe Sinwar ka iya kawar da duk wani shinge da ke haifar da tarnaki a tattaunawar kawo karshen yakin Gaza.

Karin bayani: Gaza: Amurka ta gabatar da sabon shirin tsagaita wuta 

Kazalika, shugaban Biden da shugabannin kasashen Jamus da Burtaniya da Faransa zasu sake fitar da jadawalin tallafa wa Ukraine da karin makamai a yakin da take yi da kasar Rasha. Taron shugabannin na zuwa a daidai lokacin da shugaba Volodymyr Zelensky ya mika daftarin nasarar da ya samu a fagen daga ga kungiyar tsaro ta NATO da Majalisar Dokokin Kungiyar Tarayyar Turai a birnin Brussels.