Amurka da rikicin nukiliyar Iran
May 5, 2006Sakataren majalisar ɗinkin duniya Kofi Annan ya yi kira ga Amurka ta tattaunawa kai tsaye da ƙasar Iran domin sasantawa a game da rikicin nukiliyar ta hanyar lumana ba tare da an kai ruwa rana ba. Sakataren na majalisar ɗinkin duniya ya buƙaci samun hanyoyi na diplomasiyya domin shawo kan Iran ta dakatar da bunƙasa sinadarin na Uranium, yayin da kuma a hannu guda ya bada shawarar tabbatarwa da Iran taimakon fasaha da shaánin tsaro. Annan yace ya yi Imani ana iya warware taƙaddamar cikin ruwan sanyi. A jiya alhamis ƙasashe biyar masu wakilcin kujerar dundundun a kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniyar suka gudanar da taro domin tattaunawa a kan wani sabon daftarin kudiri da Faransa da Britaniya suka gabatar wanda ke buƙatar wajabtawa Iran ta dakatar da bunƙasa sinadarin na Uranium. Daftarin ya ambaci yin amfani da sashe na bakwai na kundin majalisar ɗinkin duniyar wanda zai iya sanyawa Iran din takunkumin karya tattalin arziki ko kuma yin amfani da karfin soji. Iran ta ce tana buƙatar masalaha idan aka cimma shawarwari bisa gaskiya da adalci.