SiyasaGabas ta Tsakiya
Amurka na son ganin an tsagaita wuta a Gaza
October 21, 2024Talla
Ma'aikatar Harkokin Kasashen Waje ta Amurkan ce ta sanar da hakan, inda ta ce zai nemi da a fara tattaunawar sulhu domin kawo karshen yakin na Gaza da ma yaduwarsa zuwa rikici a Lebanon. Wannan ne dai karo na 11 da babban jami'in diflomasiyyar na Amurka da ke zaman sakataren harkokin wajenta Antony Blinken ke ziyara a yankin na Gabaas ta Tsakiya, tun bayan harin ba-zata na ranar bakwai ga watan Oktoban bara da Hamas ta kai Isra'ila da ya yi sanadiyyar barkewar rikicin sakamakon hare-haren ramuwar gayya da kokarin tseratar da wadanda kungiyar mai gwagwarmaya da makamai a yankin Zirin gaza na Falasdinu ta yi da wasu Isra'ilawa da kuma makwabciyar kasa Lebanon domin yakar kungiyar mayakan Hezbollah da ke da alaka da Hamas din.