Amurka ta ce Edmundo Gonzale ne shugaban Venezuela
August 2, 2024Amurka ta mince da dan takarar jami'ar adawa Edmundo Gonzalez Urrutia a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben shugaban kasar Venezuela
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a cikin wata sanarwa ya ce bisa ga hujjoji kwarara da aka samu, a baiyane ta ke ga Amurka musamman jama'ar Venezuela cewa Edmundo Gonzalez Urrutia shi ne ya sami kuri'u mafi rinjaye a zaben shugaban kasar Venezuela na ranar 28 ga watan Yuli.
A ranar Litinin da ta gabata hukumar zaben Venezuela ta ayyana shugaba Nicolas Maduro a matsayin wanda ya lashe zaben, lamarin da ya haifar da zanga zanga a Caracas babban birnin kasar.
Yan adawa da gwamnatocin kasashen waje sun yi watsi da sakamakon da aka fitar a hukumance. Yayin da gwamnatin ta mayar da martani da kama daruruwan yan adawar. Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Venezuela Foro Penal ta ce an kashe akalla mutane 11 a zanga zangar.