Amurka ta dage haramcin sayer wa Saudiyya manyan makamai
August 9, 2024Gwamnatin Joe Biden ta yanke shawarar dage haramcin sayer da makamai masu linzami da Amurka ta yi wa Saudiyya, kamar yadda wasu majiyoyi uku da ke da masaniya kan lamarin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a wannan Juma'a, wanda ke zama sauya manufofi na shekaru uku, a wani mataki na tursasa wa Masarautar kawo karshen yakin Yemen.
Wani babban jami'in gwamnatin Biden ya ce Saudi Arabia ta cikanta nata bangaren yarjejeniyar, kuma a shirye suke su gana da namu, tare da maido da hada-hadar gadan gadan ta hanyar sanar da majalisa da tuntubar wadanda suka dace.
A watan Maris din shekarar 2022 ne dai Saudiyya da mayakan Houthis suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta karkashin jagorancin MDD, kuma tun sannan babu wani hari da jiragen yakin Saudiyya suka sake kaiwa a Yemen, kuma an daina kai hare-hare ta kan iyaka daga Yemen zuwa cikin masarautar, in ji jami'in gwamnatin.