SiyasaGabas ta Tsakiya
Amurka ta jaddada ci gaba da kai hare-hare
February 4, 2024Talla
Kawancen dakarun Amurka da Burtaniya sun kaddamar da farmaki kan mayakan Houthi na Yeman, domin dakile hare-haren da mayakan ke kaiwa kan jiragen ruwan da ke shawagi a tekun Bahar Maliya da gabar tekun Aden.
Al'amura sun sake tsananta a yankin tun bayan kisan sojojin Amurka uku a Jordan a ranar 28 ga watan Janairun wannan shekara. A cewar ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, sojin na Amurka sun harba makamai masu linzami kimanin 85, a wurare 7 da ke kasancewa tungar mayakan Houthi Siriya da Iraqi.
Sai dai kungiyar Houthin ta ce barazanar Amurka ba zai sauya musu ra'ayi ba, na goyon bayan da suke bawa al'ummar Gaza.