1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Amurka sun hallaka wasu yan ta'adda a Somaliya

Zulaiha Abubakar
September 13, 2018

Rundunar sojojin kasar Amurka ta sanar da samun nasarar kashe wasu mayakan kungiyar Al-shabaab yayin musayar wuta tsakanin dakarun Amurka da Sojojin Somaliya da kuma mayakan 'yan ta'addan.

https://p.dw.com/p/34pV8
Somalia Kämpfer der Terrormiliz al-Shabaab
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Abdi Warsameh

Sanarwar ta kara da cewar an fara harin na hadin gwiwa ne tun cikin mako da ya gabata, a kauyen Mubaraak da ke yammacin birnin Mogadishu. Kasar Amurka dai na goyon bayan gwamnatin Somaliya a kan yaki da 'yan ta'dda, wadanda har yanzu suke rike da wasu yankunan kasar. A 'yan kwanakinnan dai mayakan na kungiyar Al-shabaab sun zafafa hare-haren kan fararen hula.