Amurka ta sake yin suka game da tsare Tymoshenko
May 14, 2012Talla
Jakadan Amurka a ƙasar ta Ukraine John Tefft ne ya ambata hakan ga manema labarai bayan wata ganawa da ya yi da uwargida Tymoshenko inda ya sake jaddada adawar Amurka game da tsare ta.
Bayan kammala ganawar, jakadan na Amurka ya shawarci mahukuntan ƙasar da su gaggauta sakinta da ma dai sauran 'yan siyasar da ake tsare da su.
Masu sanya idanu kan sha'anin siyasar Ukraine din dai na ganin tsare uwargida Tymoshenko da ake a gidan kaso abu ne da ƙarara ya ke da nasaba da siyasa saboda sa-toka-sa-katsin da ke akwai tsakanin ita Yulia Tymoshenko da shugaban ƙasar Viktor Yanukovych.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Zainab Muhammad Abubakar