Sakon taya murnar Amurka ga Tinubu
March 2, 2023A waje guda kuma fadar White House ta yi kira ga 'yan Najeriya da su kwantar da hankula bayan zarge-zargen magudi da matsaloli da aka fuskanta yayin zaben.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana sakon taya murnar ne a lokacin da yake ganawa da takwaransa na Najeriya Geoffrey Onyeama a wajen taron kasashe masu ci gaban masana'antu na G20 da ake yi a birnin New Delhi na kasar Indiya.
A cikin wata sanarwa, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce tana sane da korafin 'yan Najeriya da wasu jam'iyyun siyasar kasar suka bayyana kan damuwarsu game da zaben.
A waje guda kuma zababben shugaban na Najeriya Bola Ahmed Tinubu wanda ya yi alkawarin hada kan 'yan kasar ya yi kira ga jam'iyyun adawa da su manta da banbance-banbancen dake tsakaninsu su hada hannu don ciyar da kasar gaba.