Amurka ta zargi rundunar RSF da aikata kisan kiyashi a Sudan
January 8, 2025Sakataren harkokin wajen Amurkar Antony Blinken, ya ce an dauki matakin ne ganin yawan kashe-kashen maza manya da yara tare ma da munin fyade da mayakan RSF din ke yi wa mata da 'yan mata kabilu a yankin Darfur.
A cewar Amurkar, takunkumai sun hau kan tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan din Mohammed Hamdan Daglo saboda jagorantar rundunar da ta aikata wannan danyen aiki a kan 'yan aksar Sudan.
Ita ma ma'aikatar baitul malin Amurka ta sanar da matakin takunkuman a kan Mohammed Daglo.
Ba kasafai ba ne dai ma'aikatar harkokin wajen Amruak ke ayyana mataki kan abin da ya danganci zargi na kisan kiyashi, a cewar Antony Blinken.
Dubban mutane ne dai, galibi fararen hula suka salwanta a yakin kasar ta Sudan, tare da wasu miliyoyin da suka rasa sukuni.