Amurka za ta karawa Iran takunkumi
March 31, 2012Amurka ta ce a shirye take ta sake tsaurara matakai na matsin lamba a kan Iran. A wani jawabin da shugaba Barack Obama ya gabatar ranar juma'a, shugaban ya ce kasarsa zata cigaba da kakaba takunkumi kan kasashen da ke sayen man fetur daga Iran.
Burin wannan mataki, shine ya mayar da babban bankin Iran saniyar ware kasancewar ita ke kula da kudaden da kasar kan samu wajen cinikin man fetur din nata a kasuwannin kasa da kasa.
Shi dai shugaba Obama ya bada amincewarsa da wannan mataki ne, bayan da ya tabbatar cewa akwai wadatar man fetur daga wasu kasashen a kasuwannin kasa da kasa, domin kada takunkumin ya janyo hauhawar farashin man.
Ana dai sa ran wannan mataki da Amurkan ta dauka, zai tallafawa yunkurin da kasashen ketare ke yi na shawo kan gwamnati a Tehran da ta dakatar da shirinta na makamashin nukiliya wanda kasashe da dama ke fargabar cewa makaman kare dangi take sarrafawa. To sai dai har wa yau Tehran ta hakikance kan cewa shirin makamashin nukiliyar nata na dalilan zaman lafiya ne.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Usman Shehu Usman