Amurka za ta shiga tsakanin bangarorin Sudan
July 24, 2024Tattaunawar da Amurka za ta jagoranta, za ta gudana ne a Switzerland a ranar 14 ga watan Augusta, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da sauran wasu manyan jami'an diplomasiyar Amurka za su kasance daga cikin masu shiga tsakani.
Shugaban rundunar RSF Mohamed Hamdan Daglo ya amsa goron gayyatar tataunawar, inda ya tabbatar da halartar wakilan bangarensa.
A baya an gudanar da tattaunawa makamanciyar wannan a birnin Jedda na Saudi Arabia a kokari na kawo karshen wannan yaki amma hakar bata cimma ruwa ba.
An shafe sama da shekara guda ana gwabza kazamin fada a tsakanin sojojin da ke karkashin babban hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun kar-ta-kwana na RSF karkashin jagorancin Mohamed Hamdan Daglo.
Dubban mutane ne wannan rikicin ya yi sanadiyan salwantar rayukansu yayin da sama da mutum miliyan 10 rikicin ya kuma raba da matsugunnensu.
Karin Bayani: Rabin al'umar Sudan na fama da ja'ibar yunwa