SiyasaJamus
An afka wa 'yan adawa a Tanzaniya
September 4, 2021Talla
Sabon matakin 'yan sandan na Tanzaniya, ya zo ne sakamakon yadda wasu daga yankin ke kiraye-kirayen sake fasalta tsarin mulkin kasar.
Kamen na yau Asabar, ya shafi wasu mutum tara da aka ce su ne suka kitsa gangamin, wanda suka ce kokari ne na kunna wutar kiyayya a kasar ta Tanzaniya.
Shugaban 'yan sandan kasar, ya ce ba za su nade hannu suna kallon wasu na kokarin tayar da husuma a kasar ba.
A baya-bayan nan ma dai gwmanatin Shugaba Samia Suluhu Hassan, ta kama jagoran adawar kasar Freeman Mbowe, wanda aka zarga da laifin ta'addanci.